Ƴansanda sun kama fasto bisa zargin sace 'yan mata

 Rundunar ’yansandan Jihar Edo ta kama wani fasto mai suna Nicholas Nusa, dan  shekara 50, bisa zargin sace ’yan mata biyar.Rundunar ta 'yan sanda  ta ce, ana kuma zargin faston da yi wa wata yarinya mai shekaru 15 ciki.



A cewar ’yan sandan, yarinyar ta haihu ta hanyar tiyata, kuma a halin yanzu tana karɓar kulawar malaman lafiya.

Binciken farko da rundunar ta gudanar ya nuna cewa an sace yaran ne a lokuta daban-daban tsakanin watan Satumban shekarar 2025 da Afrilu 2026.

Rundunar ta ce wanda ake zargin ya amsa aikata laifin yayin gudanar da bincike. Sai rundunar ta ƙara da cewa, tana ci gaba da ƙoƙarin gano yadda za a mayar da yaran ga iyalansu, yayin da bincike kan lamarin ke ci gaba.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org