EFCC Ta Cafke Tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman.

 Hukumar Yaƙi da Yi Wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta sanar da kama tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, bayan shafe wani lokaci yana ɓuya sakamakon hukuncin ɗaurin shekaru 75 da kotu ta yanke masa.


Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a hedikwatar hukumar.


A cewarsa, jami’an hukumar sun samu nasarar cafke tsohon ministan ne a unguwar Rigasa da ke jihar Kaduna da misalin ƙarfe 3:30 na daren Talata, bayan wani bincike da bibiyar sawunsa da aka daɗe ana yi.


Rahotanni sun nuna cewa kama Mamman ya zo ne bayan ya shafe lokaci ba a ganin sa tun bayan hukuncin da aka yanke masa kan zarge-zargen da suka shafi almundahanar kuɗi da cin hanci.

Olukoyede ya ce jami’an EFCC sun gudanar da aiki na musamman kafin su samu nasarar gano inda tsohon ministan yake tare da kama shi ba tare da wata matsala ba.


Hukumar ta ce za ta fitar da ƙarin bayanai kan yadda aka gudanar da samamen kama shi da kuma matakan shari’a da za a ɗauka a gaba.



Saleh Mamman ya taba riƙe muƙamin Ministan Wutar Lantarki a gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kafin daga bisani a gurfanar da shi kan wasu tuhume-tuhume masu alaƙa da karkatar da kuɗaɗen gwamnati.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org