Ministan Gidaje injiniya Muttaka Rabe Darma Ya Biya Wa Dalibai 33 Kudin Jarabawar Neco A Makarantar Mata Ta W.T.C A Katsina

Ministan Gidaje da bunƙasa birane Hon. Dakta Injiniya Muttaqha Rabe Darma ya biya Naira miliyan 1,072,500 ga ɗalibai 33 da suka kasa shiga cikin tsarin wadanda gwamnati ke biya mawa kuma basu da karfin biya ma kansu a makarantar WTC da ke Katsina.



Mai Taimaka masa na musamman (PA) Gambo Garba ne ya jagoranci miƙa kuɗin ga shugabar Makarantar ta WTC domin biyawa ɗaliban kudin jarabawar.


Gambo Garba ya jaddada cewa, Ministan Gidajen ya biya kuɗin ne, biyo bayan roƙo da Shugabar Makarantar Sakandare ta WTC Hajiya Hadiza Nasir tayi ga Ministan kan ya taimakawa daliban domin basu da ikon biya ma kansu.


A dalilin wannan roƙo da suka yi, Ministan ya tura mai taiimka masa (PA)  Gambo Garba domin kai waɗannan kuɗaɗe.


Da take jawabi, Shugabar Makarantar Hajiya Hadiza Nasir ta gode wa Ministan kan wannan taimako da ya yiwa ɗaliban, tana mai addu'a ga Allah da ya saka mashi da alheri. Haka zalika, ta kuma nemi alfarma ga Ministan da a ci gaba da taimakawa a duk lokacin da aka buƙaci taimako daga gare shi.


A jawabin su, Ɗaliban sun godewa Ministan kan taimakon rayuwar su, tare da addu'a ga Allah da ya yi jagoranci a gare shi gami da yi mashi jagoranci.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org