EFCC Ta Miƙa Wa Gwamnatin Katsina Kuɗaɗen da Ta Kwato Naira Miliyan 837

Hukumar Yaƙi da Masu Yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa ta EFCC reshen Kano ta miƙa wa Gwamnatin Jihar Katsina kuɗaɗen da ta kwato da suka kai Naira miliyan 837 da dubu 485.

Kuɗaɗen sun haɗa da sama da Naira miliyan 547 da aka gano an karkatar daga harajin wasu ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa kamar WHO, MSF da ALIMA, inda aka zargi jami’an Hukumar Tara Haraji ta jihar da wasu ma’aikatan banki da hannu a lamarin.


Haka kuma EFCC ta ce ta ƙwato Naira miliyan 290 da ake zargin wasu tsofaffin jami’ai a ofishin Akanta Janar na jihar sun karkatar ta hanyar cire kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba.


Daraktan EFCC na shiyyar Kano, ACE1 Friday S. Ebelo, ne ya miƙa kuɗaɗen ga Daraktan Tsare-tsare da Bincike na Hukumar Tara Haraji ta Katsina, Dr. Kabir Abdullahi Yantumaki, a Kano ranar Litinin.


Ebelo ya ce EFCC za ta ci gaba da bin diddigin masu wawure dukiyar jama’a, yayin da Yantumaki ya tabbatar da cewa za a sanya kuɗaɗen cikin asusun gwamnatin jihar domin amfanin al’umma.


Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org