DA ƊUMI-ƊUMI: Tsawa Ta Kashe Jami'in Ɗan Sanda Har Lahira a Jihar Borno
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Borno ta tabbatar da rasuwar wani sifetan ‘yan sanda, Abdulkadir Garba, wanda aka fi sani da “Buratai,” bayan wata guguwa mai tsawa ta kashe shi yayin da yake bakin aiki a Maiduguri, babban birnin jihar
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, ASP Nahum Daso, a wata sanarwar ta’aziyya da ya fitar ranar Juma’a, ya ce an buge jami’in da tsawa a ranar Laraba tare da babban abokin aikinsa, ASP Wazani Adamu, wanda ya tsira daga lamarin.
A cewarsa, jami’an biyu sun yi ƙoƙarin neman mafaka kafin ruwan sama ya fara, amma tsawar ta same su kafin su isa inda suke nufi.
