Sufeto-janar na ’yan Sandan Najeriya, ya umarci da a gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa wasu manyan jami’an ’yan sanda biyu.
sufeto-janar na ’yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu ya umarci sashin sa ido na rundunar da su gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa wasu manyan jami’an ’yan sanda biyu, CSP Hussaini Gimba da CSP Hassan Gimba.
Za a yi binciken dangane da ɓacewar da kuma zargin kisan Abubakar Idris, wanda aka fi sani da Dadiyata.
Wannan umarni ya biyo bayan jerin ƙorafe-ƙorafe da wani mai fafutuka kuma lauya mai kare haƙƙin ɗan Adam mazaunin Kano, Abba Hikima ya gabatar a ranar Juma’a.
Takardun ƙorafe-ƙorafen, waɗanda wakilinmu ya gani kuma aka aika wa Sufeto-Janar, sun jawo hankali ne kan wasu iƙirari da Muhammad Musa Kamarawa ya yi.
Kamarawa wanda tsohon babban mataimaki ne na musamman ga tsohon gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle.
Kamarawa ya yi zargin cewa jami’an sun taɓa yi masa barazana, inda suka gaya masa cewa sun kashe Dadiyata da wasu mutane a gabansa a ofishin rundunar Operations Yaki da ke Kaduna.
A ɗaya daga cikin takardun ƙorafin, lauyan ya jaddada cewa idan har zargin na bogi ne, bincike na gaskiya zai wanke sunan jami’an.
To sai dai idan gaskiya ne, sun bayyana cewa dole ne a tabbatar da adalci "ba tare da duba matsayin ofis, ko tasirin wanda ake zargi ba."
Takardun sun nuna damuwar da al’umma ke ciki kan ɓacewar Dadiyata tun watan Agustan shekarar 2019, sannan suka buƙaci kafa kwamitin bincike mai zaman kansa.
Yayin da yake tabbatar da karɓar takardun ƙorafin, Sufeto Janar (IGP), ta hannun babban jami’in ma’aikatansa (PSO), CF Lateef Adio Ahmed ya tabbatar da cewa an tura maganar zuwa ga Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda (DCP) mai kula da sashin sa ido domin ɗaukar matakin gaggawa.
Wasikar ta tabbatar wa masu ƙorafin ƙudurin rundunar na tabbatar da adalci da kuma yin bayani kan duk wani abu da ya faru.
Dadiyata, malami ne a jami’a kuma mai fafutuka a kafofin sada zumunta, wanda aka yi garkuwa da shi daga gidansa da ke Barnawa, a Kaduna tun a watan Agustan 2019.
