Zargin cin hanci: Kotu ta ɗage shari’ar El-Rufai

 Babbar kotun tarayya da ke Kaduna ta ɗage sauraron shari’ar cin hanci da rashawa da ake yi wa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, zuwa ranar 1 ga Yuni, 2026.


Hukumar ICPC ce ke tuhumar El-Rufai da zargin almundahanar kuɗi yayin da yake mulki, sai dai tsohon gwamnan ya musanta dukkan zarge-zargen da ake yi masa.


A zaman kotun na ranar Alhamis, lauyan El-Rufai, Mustapha Abubakar (SAN), ya shaida wa kotun cewa har yanzu bai shirya gabatar da ƙorafe-ƙorafen farko ba.


Lauyan ya bayyana cewa ƙorafe-ƙorafen na neman a soke wasu takardun da hukumar ICPC ta haɗa cikin tuhumar da ake yi wa wanda yake karewa.


Tun da farko, kotun ta bai wa El-Rufai beli kan kuɗi naira miliyan 200 tare da sharadin mutane biyu da za su tsaya masa.


Kotun ta ce ɗaya daga cikin masu belin dole ne ya kasance babban ma’aikacin gwamnati mai matsayi na Gm 15 ko sama da haka, yayin da ɗayan kuma zai kasance fitaccen dattijo daga jihar Kaduna.


Sai dai kotun ta yi watsi da buƙatar amfani da garantin banki maimakon ajiya na kuɗi ga ɗaya daga cikin masu belin.


Haka kuma, kotun ta amince da sauya sharadin mutum na biyu, inda yanzu shugaban gunduma zai iya tabbatar da shi maimakon Majalisar Dattawan Kaduna.

Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org