Bldr. Muazu Ya Yaba Wa Gwamna Radda Education Vision, Yace Makarantar Model Za Ta Samar Da Wakilan Canji
Shugaban Kamfanin USMAHUF Ventures Ltd kuma babban mai ba da shawara ga Makarantar Sakandare ta Radda Model, Bldr. Usman Muazu, PhD ya yaba da kaddamar da Makarantar Sakandare ta Radda Model mai miliyoyin naira a yankin Karamar Hukumar Charanchi
A cewar Muazu, cibiyar tana wakiltar irinta ta farko a Arewa kuma an tsara ta ne don sake fasalin ingantaccen ilimi a duk fadin yankin.
"Wannan makarantar za ta samar da wakilai masu kawo sauyi a dukkan fannoni na rayuwa," in ji mai ba da shawara.
Bldr. Muazu ya yaba wa Gwamna Malam Dikko Umaru Radda'a wajen kafa makarantu masu wayo a wurare da dama a jihar.
"Burin Gwamna abin yabawa ne. Ana kafa wadannan makarantu ba wai kawai a Radda ba, har ma a Durmukul da Jikamshi," in ji shi.
Muazu ya ƙara jaddada cewa ilimi a ƙarƙashin Gwamna Radda yana fuskantar juyin juya hali, yana mai ƙara da cewa jihar tana da sa'a da samun shugaba mai aiki tuƙuru a Radda.
