Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke zamanta a unguwar Danbare a Jihar Kano, ta gurfanar da wani mutum mai suna Malam Shaddadu bisa zargin sayar da gidan ɗansa ba tare da izini ba.
Ɗan mutumin wanda ya gabatar da ƙara, Muhammad Shaddadu, ya shaida wa kotu cewa, lamarin ya samo asalin ne tun bayan da mahaifinsa ya saya wa wasu ‘yan uwansa biyu da suke uba ɗaya babura masu kafa uku da aka fi sani da Adaidata Sahu.
Sai dai daga baya, tsautsayi ya rutsa da ɗaya daga cikinsu wanda ɓata-gari suka kai masa hari har suka kashe shi, kuma suka yi awon gaba da babur din nasa.
Muhammad ya bayyana cewa kwatsam sai mahaifinsa ya ɗora masa alhakin faruwar lamarin, inda ya kai shi har gaban kotu kuma aka tsare shi a gidan yari.
Amma daga baya kotu ta wanke shi daga tuhumar da ake yi masa, kuma bayan ya dawo gida, ya gano cewa mahaifinsa ya sayar da gidansa, bisa zaton cewa ba zai dawo ba.
Yayin da aka karanta masa ƙunshin tuhumar a kotu, mahaifin ya musanta zargin, yana mai cewa ba shi da laifi.
Jaridar Aminiyya ta ruwaito cewa alƙalin kotun, Malam Munzali Idris Gwadabe, ya bayyana lamarin a matsayin rikicin cikin gida tsakanin uba da ɗa, inda ya miƙa shari’ar zuwa kotun sasanci domin ta jiɓanci taƙaddamar da ke tsakanin ɓangarorin biyu.
