"Bana buƙatar sai Allãĥ Ya ce ga abin da zan yi".Cewar Bilkisu Nasir Elrufa'i


Bilkisu El-Rufai ta ce ta isa kanta, ba ta buƙatar izinin kowa face na Ubangiji – ta kuma tabbatar da matsayin ta a bainar jama’a.



A wani bidiyo da ta wallafa a shafinta na Instagram, Bilkisu Malam Nasir El-Rufai ta bayyana cewa ta fi son rayuwa cikin natsuwa ba tare da tasirin kowa a kan ra’ayinta ba. Ta ce:

 “Ba ku da wani tasiri ko amfani a rayuwata. Ni ba ma cika magana saboda kar wani ya dauka yana da iko a kan ni. Abin da zan yi sai Allah Ya ce.”



A cikin wannan sanarwa, Bilkisu ta kuma yi karin haske game da kanta, inda ta bayyana kanta a matsayin mai kare ’yan luwadi da madigo (LGBTQ advocates). Wannan furuci ya samu martani iri-iri a shafukan sada zumunta, yayin da wasu ke nuna mamaki, wasu kuma na bayyana rashin yardarsu da irin wannan matsayi.

Rahoton ya fito daga Dokin Karfe TV, tare da jaddada cewa maganganun nata sun tayar da mahawara mai zafi tsakanin al’umma, ganin yadda al’amuran irin wannan ke da karfi na zamantakewa da addini a Najeriya.




#NigeriaNews #BilkisuElRufai #SocialMediaReactions #ArewaNews #TrendingNaija #HausaUpdates #DokinKarfeTV

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org