Matasa a Ostiraliya sun garzaya Kotu domin hana dokar hana Social Media.
Wasu matasa ‘yan ƙasar Australia sun shigar da ƙara a gaban High Court domin dakatar da dokar da gwamnatin ƙasar ke son kafa wa, wacce za ta haramta amfani da kafofin sada zumunta ga matasa ƙasa da shekaru 16.
Lauyoyin matasan sun ce dokar:
Ta sabawa ‘yancin mutum na samun bayanai
Ta tsoma baki cikin rayuwar matasa
Kuma ba ta magance matsalar tsaro yadda ya kamata
Gwamnati dai ta ce manufarta ita ce kare yara daga cutarwa, cin zarafi da barazanar intanet, amma masu adawa na ganin hakan gabaɗaya takurawa ne da zai iya cutar da ilimi, hulɗa, da ci gaban matasa.
Shari’ar na iya zama mafi girman gwaji ga matsayin ‘yancin amfani da social media a duniya, kuma dukkan idanu sun zuba zuwa kotu domin ganin hukuncin da za ta yanke.
#Australia #Matasa #SocialMediaBan #HighCourt #HumanRights #DigitalRights #YouthVoices #WorldNews #TechPolicy #HausaNews