An samu ragin rarraba kwaroron roba a Najeriya da kashi 55%.UNAIDS
A sabon rahoton da hukumar UNAIDS ta fitar, an bayyana cewa Najeriya ta fuskanci mummunan raguwar rarraba kwaroron roba da kashi 55%, abin da masana ke ganin zai iya kara barazana ga yaduwar cututtukan da ake dauka ta jima’i — musamman HIV/AIDS.
Hukumar ta ce raguwar ta samo asali ne daga:
Karancin tallafin da ke zuwa daga ƙasashen waje,
Tattalin arzikin gida da ya yi rauni,
Ƙaruwar farashin kayayyakin lafiya,
Da kuma ƙarancin kamfen ɗin wayar da kai a matasa.
Masana sun yi gargadin cewa wannan koma-baya na iya kawo haɗari matuƙa, domin Najeriya na daga cikin ƙasashen da ke da yawan matasa masu shiga haɗarin daukar cututtuka saboda rashin isassun kayan kariya.
#Nigeria #UNAIDS #HealthNews #Lafiya #HIVPrevention #YouthAwareness #SexualHealth