Yadda Ministan Tsaro Matawalle Ya Mika Daliban Maga da Aka Ceto Zuwa Hannun Gwamnan Kebbi



A yau, Ministan Tsaron Najeriya, Bello Muhammad Matawalle, ya mika daliban GGCSS Maga da aka ceto ga Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris, a babban birnin tarayya Abuja.

An ceto dalibai mata 25 ne bayan haɗin gwiwar Ofishin Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan Tsaro (NSA), Hukumar Tsaro ta DSS, da sauran jami'an tsaro. Rahotanni sun tabbatar da cewa an fitar da su cikin koshin lafiya daga hannun masu garkuwa.

Gwamna Nasir Idris ya yaba da kokarin jami’an tsaro tare da nanata cewa gwamnati za ta cigaba da amfani da duk wani karfi da doka ta basu domin kare rayuwar ‘yan jihar, musamman dalibai.

Matawalle ya jaddada cewa gwamnatin tarayya tana kan bakin alkawarin ta na kawowa Najeriya karshen garkuwa da mutane, tare da tabbatar da tsaro a makarantu.




#Kebbi #DalibanMaga #TsaroNigeria #Matawalle #NasirIdris #GarkuwaDaMutane #NSA #DSS #Najeriya #EducationSafety #BreakingNews #DaDumiDumi

Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org