Tsohon Gwamna Yana Fuskantar Bincike Kan Zargin Daukar Nauyin Yunƙurin Juyin Mulki a Nigeriya
Wani tsohon gwamnan Najeriya yana fuskantar bincike daga Hukumar Leƙen Asirin Soji ta Ƙasa (DIA) bisa zargin daukar nauyin wasu sojoji da ake zargin suna shirin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito daga majiyoyi masu tushe, tsohon gwamnan — wanda ɗan yankin Kudu ne kuma tsohon babban jami’in gwamnati a ɓangaren albarkatun mai da iskar gas — ana zarginsa da bayar da kuɗaɗen da ake amfani da su wajen shirin juyin mulki da aka shirya gudanarwa a ranar 25 ga watan Oktoba, 2025.
Majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa wannan zargi ya haifar da girgizar tsaro a cikin rundunar sojojin Najeriya, inda aka kama sojoji 16 ciki har da Birgediya Janar, Kanar, da wasu jami’an ƙanana a Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Harkokin Tsaro (NSA).
Rahotannin da Sahara Reporters da Premium Times suka wallafa sun bayyana cewa an fara cafke waɗannan jami’an ne bisa laifin karya ƙa’idar aikin soja. Amma daga bisani, bincike ya nuna cewa akwai alaƙa tsakaninsu da wani yunƙuri na kifar da gwamnatin Shugaba Tinubu.
Majiyoyin cikin rundunar sun ce hukumar DIA tana bin sawun alamu masu nuna yiwuwar hannun fararen hula a cikin shirin, musamman batun yadda kuɗi ke yawo da kuma tattaunawar da aka yi tsakanin waɗanda ake zargi da tsohon gwamnan.
Wani babban jami’in tsaro ya tabbatar wa da Aminiya cewa: “Gaskiya ne. Akwai fararen hula da ke cikin wannan lamari, ciki har da wani tsohon gwamna. Ana ci gaba da bincike don gano rawar da kowane ɗaya ya taka. A halin yanzu, sojoji 16 ne ke tsare da ake tuhuma da hannu a shirin.”
A halin yanzu, ‘yan Najeriya na jiran cikakken bayani daga hukumomin tsaro kan matsayin binciken da kuma yadda tsohon gwamnan da sojojin da ake tsare da su za su kare kansu.
Katsina Times