Zaben 2027 zai zama tamkar faɗa tsakanin talakawan Najeriya da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

 Tsohon Ministan Wasanni da Ci gaban Matasa, Solomon Dalung, ya bayyana cewa babban zaben 2027 zai zama tamkar faɗa tsakanin talakawan Najeriya da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Dalung ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da News Central, inda ya soki gwamnatin mai ci da cewa ta tsananta rayuwa ga ƴan ƙasa, ta hanyar haifar da ƙarin talauci da yunwa.


“Ko da Tinubu ya naɗa ɗansa Seyi Tinubu a matsayin shugaban INEC, kuma matarsa ta zama Babbar Alƙaliya ta Ƙasa, ba zai ci zabe ba a 2027,” in ji Dalung.


Ya ƙara da cewa hanya ɗaya da ta rage wa Najeriya ita ce haɗin kan ƴan adawa ƙarƙashin sabuwar kawancen jam’iyyun siyasa da ke karkashin tutar ADC, domin su tunkari jam’iyyar APC mai mulki a zabe mai zuwa.

“Gwamnatin Tinubu ta bayyana wa al’umma yaƙi, ta mayar da talauci da yunwa makamai. Saboda haka sai mu tashi tsaye. A 2027, sai dai mu da su. Jama’a su shirya,” in ji Dalung.

Tsohon ministan ya yi kira da a sake tsari a siyasa ta yadda talaka zai sami mafita daga matsin rayuwa da rashin adalcin shugabanni

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org