Rikicin Da Zai Iya Mamaye Jam’iyyar APC A Jihar Kano Idan Ta Hana Ɓangaren Ganduje Takarar Gwamna
Rikicin Da Zai Iya Mamaye Jam’iyyar APC A Jihar Kano Idan Ta Hana Ɓangaren Ganduje Takarar Gwamna Ta Ba Wa Ɓangaren Barau Ko Ta Hana Ɓangaren Barau Ta Ba Wa Ɓangaren Ganduje
DAGA Bashir Abdullahi El-bash
Idan muka yi duba da yadda lamuran siyasa ke gudana a yanzu, za mu iya cewa jam’iyyar APC tana cikin tsaka mai wuya musamman ta fannin fidda ɗan takarar gwamna 2027 a Jihar Kano. Domin kuwa da ɓangaren Sanata Barau Jibrin da Ɓangaren Dakta Ganduje kowa na nema.
Duba da wannan, a hasashe za mu iya cewa akwai ƙura babba idan har jam’iyyar APC ta ba wa ɓangaren Ganduje takara ta hana ɓangaren Barau ko ta hana ɓangaren Barau ta ba wa ɓangaren Ganduje.
Duba da cewa, ɓangaren Sanata Barau wanda shi ne mataimakin shugaban majalissar dattijai yanzu ne suke kan kafuwa. Amma suna da ƙarfin iko na gwamnati. Haka zalika ɓangaren Ganduje wanda shi ne tsohon gwamnan Jihar, kuma tsohon shugaban jam’iyya na ƙasa, tuntuni a kafe suke suna da jama’arsu.
Duba da wannan, za mu iya cewa idan ɓangaren Barau ba su samu takarar gwamna ba za su iya ficewa daga jam’iyyar su marawa sabuwar jam’iyyar haɗaka baya. Haka su ma ɓangaren Ganduje idan ba a ba su takara ba za su iya marawa sabuwar jam’iyyar haɗaka ta ADC baya.
Sai dai kuma, a siyasa komai na iya canzawa, lokaci ne kaɗai zai nuna.