Tinubu Zai Samar Da Ayyukan Yi Ga Matasa Miliyan Biyar A Fannin Kiwo, Cewar Farfesa Attahiru Jega

 Mai bai wa shugaban kasa shawara, kuma shugaban kwamitin aiwatar da garambawul kan harkokin kiwon dabbobi, Farfesa Attahiru Jega, ya yi gargadin cewa; Nijeriya na iya fuskantar kasadar karancin abinci mai gina jiki ga yara, idan har ba a aiwatar da tsarin sake fasalin kiwon dabbobi na gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.


Ya kuma bayyana cewa, a kokarin da ake yi na cike gibin da ake da shi a bangaren abinci mai gina jiki, Nijeriya na kashe makudan kudade da suka tasamma Naira biliyan 1.5 a duk shekara, wajen shigo da kayayyakin kiwo; wanda galibi madara ta fi yawa, wadda ke da kuma karancin sinadarin gina jiki.


Haka zalika, Jega ya ce; “Daga nan zuwa shekarar 2030, idan ya kasance an aiwatar da tsare-tsare da kuma gyare-gyare a kan kiwon dabbobi na shirin Shugaba Tinubu, Nijeriya za ta samu nasarar kirkiro ayyukan yi kusan kimanin miliyan biyar ga matasa, ta fuskar samar da wadataccen nama, kiwo, fata da sauran kayayyakin da kamfanoni ke bukata, musamman don taimaka wa matasa da mata a yankunan karkara da birane, wajen samun ayyukan yi.”


Wannan dai na zuwa ne, daidai lokacin da shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da ayyukan noma da raya karkara, Saliu Mustapha, ya ba da shawarar ware kashi 6 cikin 7 na kasafin kudin Nijeriya, domin samar da ayyukan yi a kasar.


An gudanar da laccar wannan shekara ta 2025 ne kamar yadda aka saba yi a kowace shekara, ranar Litinin da ta gabata a Jami’ar Ilorin da ke Jihar Kwara, don girmama wani dan majalisa.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org