Ina nadamar zafafan kalaman da na faɗa a kan Trump - Elon Musk

 Mamallakin Kamfanin kafar sadarwa ta X, Elon Musk ya ce wasu daga cikin sakonnin da ya wallafa a shafukan sada zumunta game da Shugaban Amurka, Donald Trump, sun yi zafi fiye da kima.


Musk da Trump sun yi musayar kalamai a makon da ya gabata — kwanaki kaɗan bayan shugaban kamfanin Tesla ya sauka daga mukaminsa a Fadar White House.


Musk ya soki dokar shugaban ƙasar mai suna “Big Beautiful Bill”, yana mai cewa za ta rushe yawancin nasarorin da ma’aikatarsa ta inganta ayyukan gwamnati (DOGE) ta cimma.


A jerin sakonnin da ya wallafa a X yayin da rikicinsu ke ƙaruwa, tsohon shugaban DOGE ya mara wa kiraye-kirayen tsige Trump baya, tare da kira shugaban ƙasar da “marar godiya” duk da taimakon da ya masa har ya samu nasarar zaɓe.


Yanzu haka yawancin waɗannan sakonnin an goge su.


A martaninsa, Trump ya ce ba shi da buƙatar maido da dangantakarsa da Elon Musk.


Trump ya bayyana cewa Musk ya nuna rashin girmamawa ga ofishin shugaban ƙasa.


Musk, wanda ya bayyana goyon bayansa ga rufe iyakoki da korar baki, ya saka tutocin Amurka a wani sako da Mataimakin Shugaban Ƙasa, JD Vance, ya wallafa kan cewa “shugaban ƙasa ba zai lamunci tarzoma da tashin hankali ba”.


Haka kuma ya saka hoto daga Truth Social inda Trump ke kira ga Gwamnan California da shugaban birnin su “ba wa mutanen Los Angeles haƙuri”.


A wata hira, Vance ya ce yana fatan Musk “zai gane gaskiya ya dawo”.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org