Alhazan Nijeriya sun yi zangza-zanga a Saudiyya.

 Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu alhazai ƴan Nijeriya sun yi zanga-zanga a  birnin Makka da ke ƙasar Saudiyya a ranar Talata, Progress Radi TV Gombe ta ruwaito.




Bayanai sun nuna cewa masu zanga-zangar suna cikin jerin waɗanda hukumomin alhazan jihohinsu suka dau nauyinsu zuwa ibadar aikin hajjin bana. 


Rahoton ya ce, lamarin ya faru ne a wani masauƙin maniyyatan ƙasar, sakamakon alawus-alawus ɗin su, da suke zargin hukumar alhazan ƙasar (NAHCON) da kuma gwamnatin Nijeriya sun riƙe. 


Ƴan Nijeriyar da suka gudanar da zanga-zangar sun fito ne daga wata ƙabila a yankin kudancin ƙasar, abin da ma ya sa wasu daga cikin mahajjatan Arewacin Nijeriyar, zargin cewa, "Zanga-zangar ba ta rasa nasaba da ƙabilanci."


"Wannan zanga-zangar ta ƙabilanci ce, saboda kawai shugaban hukumar NAHCON ba ɗan yankin su ba ne, kuma bai fito daga cikin ƙabilar su ba." 


Zuwa yanzu Hukumar Alhazan Najeriya ba ta ce komai ba kan lamarin.

Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org