Jirgin Air India Mai Dauke da Fasinjoji 242 Ya Yi Hatsari a Ahmedabad

Wani jirgin sama mallakin kamfanin Air India wanda ya nufi birnin London ya yi hatsari a birnin Ahmedabad na kasar India, jim kadan bayan tashinsa daga filin jirgin saman birnin.

 


A cewar wani rahoto da aka samu, jirgin yana dauke da fasinjoji 242 a lokacin da lamarin ya faru. Har yanzu hukumomi ba su fitar da cikakken bayani kan musabbabin hatsarin ba, kuma ba a tabbatar da adadin wadanda suka jikkata ko rasa rayukansu ba.

Ana ci gaba da aikin ceto da bincike a wajen da hatsarin ya faru, yayin da hukumomin tsaro da na kula da sufurin jiragen sama ke gudanar da bincike don gano musabbabin wannan mummunan al'amari.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org