Jihar Kano ta bukaci diyya daga Gwamnatin Tarayya bisa soke Hawan Sallah
Gwamnatin Jihar Kano ta bukaci Gwamnatin Tarayya da ta biya diyya sakamakon soke bikin Hawan Sallah na tsawon shekaru biyu a jere.
Kwamishinan harkokin kananan hukumomi da masarautu na jihar, Alhaji Tajo Uthman, ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, yayin da Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, ya kai gaisuwar Sallah ga Gwamna Abba Kabir Yusuf a fadar gwamnati.
Uthman ya ce jihar ta yi asarar kudade masu yawa sakamakon dakatar da wannan biki na al’ada da ake gudanarwa a kowace shekara, wanda a kullum ke jawo baki daga ciki da wajen ƙasa.
“Bikin Hawan Sallah an amince da shi a matakin UNESCO a matsayin wani abin tarihi. A lokacin wannan biki, Kano na samun kudaden shiga masu yawa daga bakin kasa da na cikin gida,” in ji shi.
Ya bayyana cewa tasirin tattalin arzikin da soke bikin ya haifar ya shafi kasafin kudin jihar na shekara-shekara.
Ya jaddada cewa Gwamnatin Tarayya ya zama wajibi ta dauki nauyin asarar tattalin arzikin da aka fuskanta sakamakon sokewar, tare da biyan jihar diyya yadda ya kamata.
“Lokaci ya yi da za mu bukaci diyya kan asarar da muka tafka,” in ji kwamishinan.
Uthman ya kuma bukaci a gaggauta dawo da bikin a jihar, yana mai bayyana sokewar bikin a matsayin abin takaici.