Marigayi Sheik Dakta Idris Abdul-Aziz Dutsen Tanshi Ya Bar Baya Da Dumbin Alheri

 Wasu daga cikin 'ya'yan Marigayi Sheikh Dr Idris Abdul-Aziz Bauchi (Limamin jaddada Tauhidi na Afirka) guda biyar sun kammala karatun jami'ah a Kasar Indiya.


Malam Idris ya tura 'ya'yansa maza da mata Kasar India domin su yi ilimi a fannoni na kiwon lafiyar mutane su dawo su cike wa al'ummar Musulmi gurbi.


Malam Idris ya gina Asibiti da kudin aljihunsa, ya kawo tsarin da mace Likita zata duba 'yar uwarta mace, a lokacin da ya gina asibitin ya nemi mace Likita tazo tayi aiki zai ninka mata albashi ya rasa, shine ya tura 'yar cikinsa taje tayi karatun.


Malam yau baya raye Allah Ya cika masa burinsa, ku duba fannoni na ilimin kiwon lafiya masu tsada da yaransa suka karanta a India, kuma sun kammala da sakamako mai kyau, gasu kamar haka:

👇

(1) Abdullahi Idris Abdul-Aziz ya karanta Physiotherapy 

(2) Abdul-Aziz Idris Abdul-Aziz ya karanta Doctor of Pharmacy 


(3) Muhammad Idris Abdul-Aziz ya karanta Medical Laboratory Technology 

(4) Khadijah Idris Abdul-Aziz ta karanta Nursing 

(5) Fatima Idris Abdul-Aziz ta karanta Radiology Imaging Technology

Idan ban manta ba akwai wanda ya kammala karatun MBBS, kunga asibiti guda ya hadu da Likitoci

Marigayi Malam Idris Abdul-Aziz rayuwarsa ta yi albarka, ya cike wa Musulunci gurbin da suka rasa, tabbas ba mu yi nadamar kasancewa tare da shi ba a lokacin da aka tsangwamemu saboda shi.



Yaa Allah Ka jikansa da rahama, Ka hada fuskokinmu da shi a cikin Aljannah Madaukakiya.


Daga Datti Assalafiy

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org