Jam’iyyar APC ta bayyana sabuwar haɗakar jam’iyyun adawa da suka rungumi ADC a matsayin “ƙungiyar ƴan yaudara

 Jam’iyyar APC ta bayyana sabuwar haɗakar jam’iyyun adawa da suka rungumi ADC a matsayin “ƙungiyar ƴan yaudara da masu bin son ransu,” tana mai cewa burinsu kawai shi ne sake mallakar mulki don biyan bukatunsu na ƙashin kansu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar ta ƙasa, Felix Morka, ya fitar a ranar Alhamis, ya ce “ƙaddamar da ADC a matsayin sabuwar haɗakar adawa ba ta kawo wani sabon fata ba face ɗaurewar bakin waɗanda suka yi fice wajen yaudarar jama’a da yaƙi da gaskiya.”


Ya ce ko da yake gwamnatin Tinubu na fuskantar ƙalubale a wasu fannoni, amma tana da nasarori masu yawa da suka janyo yabo daga ƙasashen waje da masana harkokin tattalin arziki.


Morka ya ci gaba da cewa: “wannan haɗaka ba ta da wata tsari ko aƙida, illa kawai neman mulki da gaggawa. Ba su da wani shiri na ci gaban ƙasa sai zagin gwamnatin Tinubu da neman dawo da kansu kan karagar mulki.”


Ya ce maganar Sanata David Mark, shugaban rikon kwarya na ADC  “ta cika da zarge-zarge marasa tushe da kuma ci gaba da yayata ƙarya kan gwamnatin da ke mulki.”


Jam’iyyar APC ta ce gwamnatin Tinubu ta kawo sauye-sauye masu amfani, ta tabbatar da ci gaba a fannonin tattalin arziki, tsaro, lafiya da ilimi, tana mai cewa: “masu adawa na ƙaryata waɗannan nasarori ne kawai saboda kishin mulki da son rai, ba domin jin daɗin talaka ba.”


Jam’iyyar ta kuma jaddada cewa haɗakar jam’iyyun adawa ba za ta iya ruɗin ƴan Najeriya ba, saboda su na da wayewa da fahimtar masu yi musu ƙarya da masu da’a ga ƙasa

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org