’Yan sanda sun kaddamar da farautar masu garkuwa da mutane bayan sace Sarkin Dari a jihar Nasarawa
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace wani basarake a ƙaramar hukumar Kokona da ke Jihar Nasarawa, wanda aka bayyana sunansa da Emmanuel Omanji.
Basaraken, wanda kuma aka fi sani da Sangarin Dari, an sace shi ne daga fadarsa da ke yankin Dari, hedikwatar ƙaramar hukumar Kokona, tsakanin karfe 11 na dare zuwa 11:30 na daren Laraba.
Wani ganau ya tabbatar da cewa ’yan bindigar sun mamaye yankin cikin yawan gaske, inda suka fara harbe-harbe a iska domin tsoratar da jama'a kafin su tafi da basaraken.
> “Masu garkuwar sun shigo fada suna harbi ba kakkautawa domin tsoratar da mutane, sannan suka tafi da sarkin,” in ji Kwamishinan Ilimi na Jihar Nasarawa, Dr. John Mamman, cikin wata tattaunawa da manema labarai ta wayar tarho.
Tuni Kwamishinan ’Yan sanda na jihar, Shetima Jauro Mohammed, ya kaddamar da tawaga ta musamman don gudanar da Aikin gaggawa na ceto, inda aka haɗa jami’an sashin yaƙi da garkuwa da mutane, sojoji da kuma ‘yan sa-kai domin gano inda sarkin yake da kuma cafke waɗanda suka aikata laifin.