INEC Ta Saki Jadawalin Zaɓen Gwamna Na Jihohin Ekiti Da Osun Na Shekarar 2026
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sanar da ranar da za a gudanar da zaɓukan gwamna a jihohin Ekiti da Osun a shekarar 2026, tare da jadawalin yadda za a gudanar da zaɓen fidda gwani na jam’iyyun siyasa.
A cewar sanarwar da hukumar ta fitar, zaɓen gwamna na Jihar Ekiti zai gudana ne a ranar Asabar, 20 ga Yuni, 2026. INEC ta ce zaɓukan fidda gwani na jam’iyyu za su gudana daga ranar 20 ga Oktoba, 2025, zuwa 10 ga Nuwamba, 2025.
A Jihar Osun, hukumar ta ce zaɓen gwamna zai gudana a ranar Asabar, 8 ga Agusta, 2026, yayin da za a fara gudanar da zaɓen fidda gwani daga 24 ga Nuwamba, 2025, zuwa 15 ga Disamba, 2025.
INEC ta bayyana cewa an tsara jadawalin ne domin bai wa jam’iyyun siyasa isasshen lokaci su shirya tare da bin dukkan ƙa’idojin da doka ta tanada wajen gabatar da 'yan takararsu cikin lokaci.
Hukumar ta kuma jaddada aniyarta na tabbatar da sahihanci, gaskiya da adalci a dukkan matakan zaɓe.