Da Dumi-Dumi: Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Soke Hukuncin Babbar Kotun Tarayya a Kan Zaɓen Kananan Hukumomi a Kano

 Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta rushe hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Kano ta yanke a kan zaɓen kananan hukumomi a jihar, inda ta bayyana cewa kotun tarayyar ba ta da hurumin sauraron shari'ar da ta shafi batun gudanar da zaɓen



Premier Radio ta rawaito cewa tun da farko, jam’iyyar APC tare da wasu mutane ne suka shigar da ƙara gaban babbar kotun tarayya domin neman dakatar da zaɓen, bisa zargin cewa shugaban hukumar zaɓe ta jihar Kano na da alaka da jam’iyyar NNPP, wadda ke mulkin jihar.

Sai dai a hukuncin da mai shari’a Oyewumi ya karanta, ya bayyana cewa kotun tarayyar ta ƙetare  iyakar huruminta wajen sauraron ƙarar, balle har ta yanke hukunci a kai. Bisa haka, kotun ɗaukaka ƙara ta amince da ƙorafin da gwamnatin jihar Kano ta gabatar, tare da soke hukuncin babbar kotun.

Wannan hukunci na nufin zaɓen kananan hukumomin da aka yi a jihar zai ci gaba da kasancewa halastacce a idon doka, inda  kuma shugabannin ƙananan hukumomi da kansilolin su za su ci gaba da zama akan kujerun su na mulki.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org