Za a Shirya Taro da Yan Sanda da Sarakuna da Mutanen Gari Domin Murkushe 'Yan Daba a Jihar Kano
An shirya taron masu ruwa da tsaki a Kano domin tattauna hanyoyin dakile rikice-rikicen daba a tsakanin matasa a yankunan jihar Masu unguwanni, dattijai, da kwamitocin tsaro sun yarda da yin aiki tare da 'yan sanda wajen gano masu haddasa rikice-rikicen Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta yi alkawarin ci gaba da daukar matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyi
Jihar kano -A ranar 11 ga Disamba, 2024, aka gudanar da taron masu ruwa da tsaki a hedkwatar rundunar ‘yan sandan Kano domin samo hanyar murkushe 'yan daba. Taron ya samu halartar shugabannin unguwanni, dattijai, da mambobin kwamitocin tsaro daga yankunan Kofar Mata, Zango, Zage, Yakasai A, Yakasai B, Fagge da wasu unguwannin Kano.
Kakakin 'yan sanda, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya wallafa a Facebook cewa an cimma matsaya kan yadda za a tabbatar da zaman lafiya da tsaro jihar.