Wani Jigo A Jam'iyyar PDP Ya Roki Tinubu ya Sauke Farashin Fetur Zuwa N300 Saboda Kirsimeti.

 Jigon PDP ya buƙaci Tinubu ya rage farashin mai na watanni 2, Disamba da Janairu.

A cewarsa, ƴan Najeriya za su ma shugaban ƙasa ruwan addu'a idan ya yi hakan.

An buƙaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya dawo da farashin man fetur N300 domin ƴan Najeriya su yi kirsimeti cikin farin ciki Tsohon mataimakin shugaban PDP na ƙasa, Bode Gearge ne ya yi wannan kira, ya ce Tinubu na iya fito da tsarin neman tallafin rage farashin Jigon PDP ya buƙaci sauke farashin daga nan zuwa watan Janairu, 2025, inda ya ce magidanta za su yi wa shugaban kasa addu'a idan ya sauƙaƙa masu 

Abuja - Tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Cif Bode George, ya yi kira ga shugaban kasa, Bola Tinubu da ya rage farashin man fetur a lokacin kirsimeti. Bode George ya roƙi Shugaba Tinubu ya tausaya ya sauke farashin litar man fetur daga sama da N1,000 zuwa N300 kacal a tsakanin watannin Disamba da Janairu. 


A cewarsa, dawo da litar mai N300 zai taimakawa ƴan Najeriya su yi bukukuwan kirsimeti cikin walwala da farin ciki, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org