Kotu a Landan ta ci tarar wani mutum £833 bisa jefar da filtar taba sigari a kasuwa

 An ci tarar wani mutum fam £833 bayan da ya jefar da filtar taba sigari a kasuwa a birnin Landan da ke kasar Birtaniya.

Tun a ranar 3 ga Disamba Carl Smith, daga New Addington a lardin Croydon da ke Kudancin Landan ya gurfanar a Kotun Majistire ta Bromley bayan ya ƙi biyan tarar da aka sanya wa duk wanda ya aikata kaifi irin nasa bayan ya jefar da filtar sigari a farfajiyar kasuwa a unguwar ta Baromley a ranar 23 ga watan Mayu.

Sai dai kuma ya masa laifinsa, wanda ya 

Mm mm mm mm

saɓa da sashe na 87 na kundin dokokin kare muhalli na 1990, inda Kotun ta ce sai ya biya fam 833.

Kotun ta yi masa bayanin cewa da farko zai biya tarar fam 293 da ake yi wa duk wanda ya aikata irin wannan laifin, sannan zai biya tarar kin biya da wuri har guda biyu da dan 423 da kuma ɗan 117.

BBC World Service ta rawaito cewa wanan shine karo na 12 da kotun ta Baromley ta yi Shari'a irin wannan laifi tun daga farkon watan Satumba, inda aka ci masu laifin jumullar tara da ta kai fam dubu 6,129.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org