Kano: Sabon shugaban ƙaramar hukumar Gwale, Mojo, ya yi barazanar sauka daga kujerarsa
Shugaban Ƙaramar Hukumar Gwale, Abubakar Muazu Mojo ya yi barazanar ajiye aikinsa na shugabancin karamar hukumar muddin ba’a sauya masa Daraktan Mulki, DPM, na karamar hukumar ba .
DAILY NIGERIAN HAUSA ta rawaito cewa tuni dai Shugaban karamar hukumar ta Gwale ya bada umarnin a rufe ofishin DPM din, Danjuma Zubairu Bebeji.
A wani sakon murya da Mojo ya aikewa manema labarai, ya yi ikirarin cewa idan har Daraktan Mulkin bai bar karamar hukumar ba to shi zai bar masa wajen .
Ya kara dacewa manufofin Daraktan Mulkin sun saɓa da tsarin Kwankwasiyya na yi wa jama’a hidima da taimako.
Rahotanni sun baiyana cewa Mojo da DPM ɗin sun jima su na takun saƙa tun lokacin da ya ke Shugaban riko na karamar hukumar ta Gwale kafin a zabe shi a watan Oktoba .
Daga cikin zarge-zargen da Mojo ke yi wa Bebeji har da yi wa karamar hukumar zagon kasa da hana tafiyar da aiki yadda ya kamata, gami da sakaci a wajen aikinsa da hakan ya janyo wasu mahimman takardu su ka ɓata.
Saboda haka ne shugaban karamar hukumar ya ce idan ba a ɗauke Bebeji ba, to shi da majalisar kansilolin sa za su sauka su bar masa wajen.
Sai dai kuma har yanzu ba a ji ta bakin DPM ɗin ba.