Sabon Shugaban Kasar Amurka Trump ya bayyana shirinsa na fatattako ‘yan Najeriya daga Amurka.
Daga Aminu Bala Madobi
Shugaban Amurka mai jiran gado Donald Trump ya sanar da shirin ayyana dokar ta-baci a kan iyakokin kasar da kuma amfani da sojojin Amurka wajen kai daukin gaggawa na korar ‘yan Najeriya da sauran ayarin ‘yan ci-rani.
Alfijir labarai ta rawaito shugaban yace batun shige da fice da daidaiton shigowar jamaa cikin kasar babban batu ne da ya dauki hankali wanda ya kasance babban abin tattaunawa ayayin yakin neman zabe.
Trump ya yi alkawarin korar miliyoyin mutane tare da daidaita kan iyaka da Mexico bayan da aka samu adadin bakin haure da suka tsallaka ba bisa ka’ida ba a lokacin gwamnatin Shugaba Joe Biden.
A jawaban da ya wallafa a shafin sa na sada zumunta na Truth Social karo na biyu, Trump ya ce “A shirye nake don ayyana dokar ta-baci kuma zan yi amfani da soji don murkushe mamaya da korar jama’a.”
Ko menene ra’ayinku???