'Yan Sanda Sun Kama Wani Dan Kasar Aljeriya Da Bindigu A Zamfara


Rundunar ‘yan sanda a jihar Zamfara ta kama wani dan kasar Aljeriya mai shekaru 58 da ake zargi da shigo da makamai cikin kasar nan, inda aka  kwato bindigu kirar AK47 guda 16, da wasu kanana biyu a hannunsa.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mohammed Dalijan ya bayyana haka a lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin a hedikwatar ‘yan sanda, da ke Gusau a ranar Talata.

Mista Dalijan ya ce ‘yan sandan sun kuma kama wasu da ake zargi da sayar da babura da harsashi ga ‘yan bindiga, dauke da tsabar kudi naira miliyan biyu da rabi.

A cewarsa, sauran wadanda aka kama sun hada da wasu da ake zargi da hakar ma'adinai ta haramtacciyar hanya.

Dalijan ya bayyana cewa, ‘yan sanda sun samu nasarar kama wadannan mutane a sassa daban-daban na jihar cikin makonni uku da suka gabata.

Ya ce ‘yan sandan sun yi aiki ne da sahihan bayanai da ke nuni da cewa ‘yan bindigar sun shirya siyan babura da dama ne a hannun wadanda aka jama.

Kwamishinan ya yi gargadin cewa, har yanzu dokar haramta hakar ma'adinai ta haramtacciyar hanya da gwamnatin tarayya da na jiha suka kafa na nan daram.

Mista Mohammed Dalijan ya jaddada cewa, duk wanda aka kama da laifin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, za a gurfanar da shi a gaban kuliya, inda ya ce, nan ba da jimawa ba za a gurfanar da wadanda aka kama.

Aminu Dalhatu

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org