Gwamnan Jigawa Ya Dage Dakatarwar Da Aka Yi Wa Kwamishinan Ayyuka Na Musamman

Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya dage dakatarwar da aka yi wa kwamishinan ayyuka na musamman Auwalu Dalladi Sankara nan take.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Jigawa Malam Bala Ibrahim ya raba wa manema labarai a Dutse.

Sanarwar ta ce dage dakatarwar ya biyo bayan sallamar kara tare da wanke sa daga laifi  da wata Kotun Shari’a ta Jihar Kano ta yi.

"Idan za a iya tunawa, an dakatar da Kwamishinan ne bisa zargin hannu a wani rahoto da aka samu a gaban Hukumar Hisbah ta Jihar Kano," Inji Sakataren Gwamnatin.

Usman Muhammad Zaria

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org