Yan Majilisar dokoki a jihar Katsina sun buƙaci gwamnatin jihar ta maida sakandire biyu na kwana

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Hon. Aliyu Abubakar Albaba ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Katsina da na ƙaramar hukumar Daura Rt Hon Nasir Yahaya Daura su ka gabatar da ƙudirin buƙatar haka a zaman majalisar ƙarƙashin jagorancin kakakin majalisar Rt Hon Nasiru Yahaya.

Haka shima ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Funtua Hon. Abubakar Muhammad Total ya gabatar da ƙudirin gyaran wasu azuzuwa da su ka lalace a makarantar firamare ta Rafin Kanya cikin mazabar Goya dake cikin ƙaramar hukumar Funtua.

Shi ko ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Batsari Hon. Mustapha Tukur Ruma ƙudiri ya gabatar yana buƙatar a samar da ababen rage raɗaɗi ga waɗanda su ka bar muhallansu a ƙaramar hukumar Batsari sanadiyar hare-haren ‘yan bindiga.

Bayan gabatar da ƙudirorin majalisar tayi doguwar tattaunawa akan ƙudirorin, kuma ta amince dasu.

Daga ƙarshe kakakin majalisar ya umurce akawun majalisar ya aikawa ɓangaren zartarwa da ƙudirin domin tayi wani abu akai.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org