Peter Obi: Arewa Na Da Damarmakin Da Najeriya Za Ta Amfana Da Su
Ɗan takarar shugaban ƙasar Najeriya na jam’iyyar NDC, Peter Obi, ya ce Arewa na da dimbin damarmakin tattalin arziki da Najeriya za ta iya cin gajiyarsu.
Obi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabijin na Arise, inda ya ce akwai manyan damar da ake da su musamman a fannin noma a yankin Arewa.
Ya ce Najeriya na da damar samun kuɗaɗen shiga masu yawa daga harkar noma, har ma fiye da abin da ƙasar ke samu daga man fetur idan aka ba fannin kulawa da jarin da ya dace.
Ya ƙara da cewa amfani da damarmakin da ke akwai a Arewa, musamman wajen bunƙasa noma, zai iya taimakawa wajen ƙarfafa tattalin arzikin ƙasa da samar da ƙarin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.
#HikayaTv #PeterObi #NDC #Arewa #Nigeria #Noma #TattalinArziki #ManFetur #NigeriaNews #HausaNews
