An binne tsohon shugaban PDP na kasa, Bamanga Tukur a Adamawa

An binne tsohon shugaban jam'iyyar PDP, Bamanga Tukur, a garinsu na Yola, Jihar Adamawa, ranar Lahadi.




An gudanar da sallar jana’izarsa bisa tsarin addinin Musulunci a Masallacin Modibbo Adama da ke Yola, inda Babban Limamin masallacin, Ahmadu Bobboi, ya jagoranci sallar da misalin ƙarfe 10:50 na safe.

Daga bisani, aka binne gawarsa a gidan iyalansa da ke Fadde-Sanda, Abuja Road, Yola.


Tukur ya rasu ne ranar Asabar a Abuja, yana da shekaru 91.

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya yi alhinin rasuwarsa, yana bayyana shi a matsayin fitaccen ɗan siyasa kuma mutum mai muhimmiyar rawa a tarihin siyasa da tattalin arzikin Najeriya.



Bamanga Tukur ya taɓa zama gwamnan tsohuwar Jihar Gongola, sannan ya riƙe muƙamin Ministan Masana’antu. Ya kuma taɓa shugabantar jam’iyyar PDP a matakin ƙasa.


Ya rasu ya bar mata biyu da ’ya’ya 18, ciki har da Sakataren Gwamnatin Jihar Adamawa, Awwal Tukur.


Daga cikin waɗanda suka halarci jana’izar akwai Aliko Dangote, Gwamnan Adamawa Ahmadu Fintiri, Sanata Iya Abbas da tsohon gwamnan jihar, Jibrilla Bindow, tare da wasu sarakuna da manyan jami’ai.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org