Iran Ta Sanar da Fitar da Jadawalin Jana’izar Ayatollah Ali Khamenei Bayan Kwanaki 132 da Rasuwarsa.
Mahukuntan Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun sanar da jadawalin jana’izar tsohon Jagoran Addinin Islama na ƙasar, Ayatollah Ali Khamenei, wadda za ta gudana na tsawon kwanaki shida daga ranar 4 zuwa 9 ga Yulin 2026, watanni fiye da huɗu bayan rasuwarsa.
A cewar sanarwar da aka fitar a hukumance, za a fara bukukuwan jana’izar ne a birnin Tehran, inda za a gudanar da tarukan ban kwana da gawarsa a Musalar Imam Khomeini a ranakun 4 da 5 ga Yuli. Bayan haka, za a gudanar da babban tattakin jana’iza a Tehran ranar 6 ga Yuli.
Haka kuma, an shirya gudanar da wasu bukukuwan tunawa da marigayin a birnin Qom ranar 7 ga Yuli, kafin a kammala da jana’iza da binne shi a Haramin Imam Reza da ke Mashhad ranar 9 ga Yuli, ɗaya daga cikin wuraren ibada mafi tsarki ga mabiya Shi’a.
Khamenei dai ya rasu ne a ranar 28 ga Fabrairu, 2026, sakamakon hare-haren sama da Amurka da Isra’ila suka kai kan Iran, yayin da gwamnatin ƙasar ta tabbatar da rasuwarsa a ranar 1 ga Maris. Rasuwarsa ta kawo ƙarshen jagorancin addinin Islama a kasar na kusan shekaru 37 a matsayin Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci, bayan da ya karɓi ragamar jagorancin a shekarar 1989 bayan rasuwar Ayatollah Ruhollah Khomeini.
A cewar rahotanni, jinkirin jana’izar tasa ta zo ne a dalilan tsaro, yanayin yaƙin da ƙasar ta shiga, da kuma shirye-shiryen sauyin shugabanci zuwa magajinsa, Mojtaba Khamenei, wanda hakan na daga cikin abubuwan da suka haddasa jinkirin.
Mahukuntan Iran sun bayyana cewa suna sa ran miliyoyin mutane daga sassa daban-daban na ƙasar da maƙwabtan ƙasashe da sauran duniya za su halarci bukukuwan jana’izar, waɗanda za su gudana a biranen Tehran, Qom da Mashhad.
Hakzalika, sanarwar jana'izar ta zo ne bayan kwanaki 132 da rasuwar Khamenei, wanda ya kasance ɗaya daga cikin fitattun jagororin siyasa da addini a tarihin Iran na zamani.
Jaridar Taskar Labarai
