Tinubu ya bar Nigeria don Kai ziyara Faransa,kenya da ruwanda.


Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, zai fara wata muhimmiyar ziyarar aiki ta mako biyu zuwa ƙasashen Faransa, Kenya da kuma Ruwanda.




Sanarwar hakan ta fito ne daga Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Tsare-tsare, Bayo Onanuga, inda ya ce shugaban zai tashi daga Abuja a ranar Asabar domin fara wannan rangadi.

A cewar Onanuga, matakin farko na tafiyar zai kasance a Faransa, kafin daga bisani shugaban ya wuce zuwa birnin Nairobi domin halartar taron haɗin gwiwar Afirka da Faransa.

Taron, wanda shugabannin Faransa da Kenya; Emmanuel Macron da William Ruto ke jagoranta, zai mayar da hankali kan batutuwa da suka haɗa da sauyin makamashi, bunƙasa masana’antu marasa amfani da fetur, sauyin dijital da kuma yaƙi da sauyin yanayi.

An tsara taron ne daga ranar 11 zuwa 12 ga watan Mayu, kuma ana sa ran halartar Shugaba Tinubu zai ƙara ƙarfafa alaƙar haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da ƙasashen Afirka da Faransa.

Taron mai taken “Africa Forward: Africa-France Partnerships for Innovation and Growth” zai zama wata muhimmiyar dama ga shugabanni da masu zuba jari domin tattauna hanyoyin bunƙasa tattalin arziki, inganta ababen more rayuwa da kuma ƙarfafa matasa da fasaha a nahiyar.

Bayan kammala wannan taro, Shugaba Tinubu zai nufi birnin Kigali domin halartar taron Africa CEO Forum na shekara-shekara daga ranar 14 zuwa 15 ga Mayu.

Taron, wanda ake gudanarwa tare da haɗin gwiwar International Finance Corporation, na daga cikin manyan tarukan kasuwanci a Afirka, inda ake haɗa shugabannin kamfanoni, masu zuba jari da masu tsara manufofi sama da 2,000.

Jigon taron na bana mai taken “Scale or Fail” zai mayar da hankali kan yadda za a hanzarta sauyin tattalin arziki ta hanyar haɗin kai tsakanin ƙasashe, da ƙara zuba jari da kuma gina masana’antu masu ƙarfi da gasa.

A yayin ziyarar, ana sa ran Shugaba Tinubu zai gabatar da jawabai a tarukan guda biyu, inda zai bayyana matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin jawo hankalin masu zuba jari da kuma inganta tattalin arzikin Nijeriya.

Haka kuma, zai gana da manyan shugabannin kasuwanci na duniya da na Afirka domin tattauna damar haɗin gwiwa.

Shugaban zai yi tafiyar ne tare da wasu ministoci da manyan jami’an gwamnati, kuma ana sa ran zai dawo Nijeriya bayan kammala ziyarar sa a Ruwanda.
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org