DA DUMI-DUMI: Peter Obi ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar ADC

 Peter Obi ya tabbatar da aniyarsa na cewa fita daga jam’iyyar (ADC), yana danganta matakin da rikice-rikicen cikin gida da ke addabar jam’iyyar.


Obi, wanda ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour Party (LP) a zaɓen 2023, ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi.

A cewarsa, ya yanke shawarar ficewa daga ADC ne sakamakon “yawaitar shari’o’i a kotuna, rikice-rikicen cikin gida, zargin juna, da kuma rabuwar kai” da ke cikin jam’iyyar.


Tun da farko, rahotanni sun nuna cewa Obi tare da Rabiu Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, na shirin barin jam’iyyar.


Matakin na Obi na zuwa ne a daidai lokacin da ake fara shirye-shiryen siyasa gabanin zaɓen 2027, lamarin da ka iya sauya fasalin haɗakar jam’iyyun adawa a ƙasar.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org