Katsina: Ƴanbindiga Sun Sace Maigarin Kogari Da Wasu Mata A Ƙaramar Hukumar Matazu.
A daren ranar Talata, 12 ga watan Mayu, 2027, wasu ’yanbindiga ɓarayin daji sun kai hari garin Kogari da ke Ƙaramar Hukumar Matazu, inda suka yi garkuwa da Maigarin garin, Bello Abdulkarim, tare da ’yarsa.
Maharan sun kuma sace matar wakilin maigarin tare da ’yarta, baya ga wasu mata biyu da suka ɗauka daga cikin garin.
Rahotanni sun ce harin ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba da tashin hankali.
Al’umma sun yi addu’ar Allah Ya kuɓutar da waɗanda aka sace cikin ƙoshin lafiya da aminci.
