Kotu Ta Yanke Wa Tsohon Ministan Wutar Lantarki Saleh Mamman Hukuncin Shekaru 75 a Gidan Yari.

 Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa tsohon Ministan Wutar Lantarki na Nijeriya, Saleh Mamman, hukuncin ɗaurin shekaru 75 a gidan yari bayan samunsa da laifukan almundahana da halasta kuɗaɗen haram da suka kai sama da Naira biliyan 33.8.


Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Ta’annati ta EFCC ce ta gurfanar da shi a gaban kotu kan tuhume-tuhume guda 12 da suka shafi karkatar da kuɗaɗe da wanke kuɗaɗen haram da ake zargin suna da alaƙa da ayyukan samar da lantarki na Mambilla da Zungeru.


Mai shari’a James Omotosho ne ya yanke hukuncin, inda ya bayyana cewa an same Mamman da laifi a dukkan tuhume-tuhumen da ake masa.


Kotun ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru bakwai-bakwai a mafi yawan tuhume-tuhumen, yayin da wasu laifukan suka jawo masa hukuncin shekaru biyu da uku.


Alƙalin ya ce hukuncin zaman gidan yarin zai kasance ne a jere, ma’ana dole ne sai an gama wa’adin hukunci ɗaya kafin a fara wani, abin da ya kai jimillar shekaru 75.


Kotun ta kuma bayyana cewa babu zaɓin biyan tara a mafi yawan laifukan da aka same shi da su, sai dai a tuhuma guda ɗaya inda aka ba shi damar biyan tarar Naira miliyan 10.


Haka kuma, mai shari’ar ya bayar da umarnin ƙwace wasu kuɗaɗen ƙasashen waje da kadarori da aka gano suna da alaƙa da tsohon ministan, ciki har da wasu manyan gidaje guda huɗu da ke Abuja.


Alƙalin ya kuma umarci hukumomin tsaro da su kamo Mamman a duk inda aka same shi domin fara aiwatar da hukuncin da aka yanke masa.


Tun a watan Yulin shekarar 2024 ne EFCC ta gurfanar da Saleh Mamman a gaban kotu bisa zargin haɗa baki da wasu jami’an ma’aikatar wutar lantarki da kamfanoni masu zaman kansu wajen karkatar da kuɗaɗen ayyukan madatsun ruwan lantarki na Zungeru da Mambilla.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org