Gwamnati Katsina ta fara duba yiyuwar gina titin jirgin ƙasa na cikin gari

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina



Gwamnatin Jihar Katsina ta fara duba yiyuwar gina titin jirgin ƙasa na zamani na cikin gari domin inganta harkokin sufuri da bunƙasa ababen more rayuwa na zamani a faɗin jihar.


A wani mataki na cimma wannan buri, gwamnatin ta kafa kwamitin ƙwararru da zai nazarci ƙudirin samar da tsarin jirgin kasa na cikin gari (Light Rail), tare da tantance yadda za a aiwatar da aikin.


Kwamitin wanda kwamishinan ayyuka na jihar ke jagoranta, ya haɗa wakilai daga muhimman ma’aikatu da hukumomin gwamnati da suka haɗa da ma’aikatar kasafi da tsare-tsare, ofishin sakataren gwamnati (SGS), hukumar tsara birane, KTDMB, KSTA, da kuma ma’aikatun filaye, muhalli, ayyuka da gidaje.


Bayanai daga gwamnatin jihar sun nuna cewa an ɗorawa kwamitin alhakin nazarin yiwuwar aikin ta fuskar fasaha da kuɗi, tare da duba yadda shirin ya dace da kundin tsare-tsaren cigaban Jihar Katsina na shekarar 2025 zuwa 2040.

Haka kuma, kwamitin zai gabatar wa gwamnati shawarwari kan anfani da muhimmancin aikin wajen haɓaka tattalin arziki da kuma rage matsalolin sufuri a jihar.

Gwamnatin ta bayyana cewa wannan yunƙuri na daga cikin manufofin Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa na samar da ingantaccen tsarin sufuri, haɗa yankuna da kuma ƙara bunƙasa cigaban jihar ta hanyar samar da manyan ababen more rayuwa na zamani.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org