Crypto Queen ta China an kamata a Landan da Bitcoin Wanda darajarsa yakai ₦10 trillion!!! Duniya fa ta ga TECHNOLOGIA.cikakken bayani👇

An kama wata fitacciyar “Crypto Queen” daga China mai suna Zhimin Qian, wacce ake kira Yadi Zhang, da ta wawuri kusan Bitcoin 61,000 — kimanin dala biliyan 6.6 (₦10 trillion!) 😱 — babban kama mafi girma a tarihin Burtaniya 🇬🇧

🔍 Ga yadda komai ya faru:

Daga 2014 zuwa 2017, Zhimin Qian ta kaddamar da babbar damfara a China ta hannun kamfaninta Tianjin Lantian Gerui Electronic Technology, inda ta janyo sama da mutane 128,000 cikin zuba jari da alkawarin riba mai tsoka. 🇨🇳

Bayan an gano damfara, ta tsere zuwa Landan ta canza suna domin ta ɓoye.

Hukumar binciken kudi ta Burtaniya ta gano Bitcoin 61,000 a hannunta — mafi girman kama na crypto da aka taba yi a kasar.

A Nuwamba 2025, kotu ta yanke mata hukuncin shekaru 11 da watanni 8 a gidan yari saboda wanke kuɗi da mallakar kadarori na damfara.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org