Zargin musgunawa: Shugaban sashin Hausa na BBC Aliyu Tanko ya yi murabus
Babban Editan sashin Hausa na BBC mafi dadewa, Aliyu Tanko, ya yi murabus, bayan zarge-zargen gallazawa daga tsohuwar ma’aikaciyar gidan, Halima Umar Saleh.
Da ya ke tabbatar da murabus ɗin nasa ga DAILY NIGERIAN, Aliyu Tanko ya ce ya yi murabus ne da bisa radin kansa bayan ya shafe shekaru 17 ya na yi wa BBC hidima cikin kwarewa.
Sai dai ya ƙi ƙarin bayani lokacin da DAILY NIGERIAN ta tambaye shi kan zarge-zargen “cin zarafi” daga tsohuwar ma’aikaciyar.
Ms Saleh, wadda a yanzu take aiki a matsayin Babbar Editar kafar yaɗa labarai ta TRT Africa, ta bayyana a wata tattaunawa da ta yi kwanan nan da Arewa24 cewa Mista Tanko ya ci zarafinta a lokacin da take aiki ƙarƙashinsa a BBC.
Wannan hirar ta jawo cece-kuce a shafukan sada zumunta bayan Arewa24 ta goge bidiyon, abin da ya haifar da zargin tsoma baki don gyaran labarai.
Wata majiya ta ce an aike da ƙorafe-ƙorafe masu yawa daga cikin gida da wajen gida zuwa hedikwatar BBC a Landan, suna neman a gudanar da bincike kan zarge-zargen.
DAILY NIGERIAN ta gano cewa Shugaban BBC West Africa, Ehizojie Okharedia, a ranar Laraba ya kira taron gaggawa, bayan haka ne Mista Tanko ya bar ofishinsa ba zato.
DAILY NIGERIAN ba ta samu tabbacin abin da ya faru a yayin taron ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.
A matsayinsa na Shugaban BBC Hausa, Mista Tanko ya jagoranci tawagar ’yan jarida da manyan ’yan jarida da ke Landan da Abuja, da kuma masu kawo rahoto daga Najeriya, Nijar, Ghana da Kamaru.