Hukumar bogi: Ban taɓa zaton haka za ta faru a Nijeriya ba - Kawu Sumaila

 Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Abdulrahman Kawu Sumaila ya baiyana al'ajabi akan zargin kafa hukumar bogi.



Da ya ke magana a BBC Hausa, Kawu Sumaila ya ce lamarin ya zubar da mutuncin Nijeriya a idon duniya.


Ya kuma baiyana mamaki akan yadda aka saka hukumar ta bogi a kasafin kuɗin Nijeriya, inda ya yi kira ga majalisar dattawan da su yi cikakken bincike don gano ƴan majalisar da su ke da hannu wajen sake kasafin kudin.


" Abin nan ya fi ƙarfin kai na. Wannan lamari ne da zai zubar da mutuncin Nijeriya a idon duniya. Amma za a iya gano su waye ke da hannu a wannan lamari saboda an saka hukumar a kasafin kuɗi.


" Shi ya sa na ke kira ga abokan aiki na sanatoci dz su yi cikakken bincike akan ya akai ma har hukumar ta samu kasafin kuɗi.


" Wannan ya na da muhimmanci domin tarihi ba a zai manta da mu ba cewa mun yi abinda ya dace ko ba mu yi ba," in ji Sanatan.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org