Majalisar dattawa ta fara binciken alawus na Naira miliyan 943 a hukumar raya yankin Arewa maso Yamma


Kwamitin majalisar dattawa mai kula da ci gaban yankuna ya fara bincike kan yadda hukumar raya Arewa maso Yamma (NWDC) ke gudanar da ayyukanta, inda ya nuna damuwa kan kashe naira miliyan 943 a matsayin alawus ga mambobin kwamitin gudanarwa.


A zaman binciken da aka gudanar ranar Talata, sanatocin sun ce matsalolin shugabanci da na gudanarwa na hana hukumar cika manufarta ta magance matsalar tsaro da gibin ababen more rayuwa a yankin Arewa maso Yamma.


Ƙaramin Ministan raya yankuna, Uba Ahmadu, ya bayyana cewa har yanzu NWDC ce kaɗai daga cikin hukumomin raya yankuna da ba ta da cikakken tawagar daraktocin zartarwa, lamarin da ya ce ya raunana ayyukanta tun bayan ƙaddamar da ita a watan Fabrairun 2025.


Ya kuma ce gwamnatin Jihar Kano ta bai wa hukumar sabon ginin ofis mai kayan aiki, motocin aiki da fili, domin kawo ƙarshen rikicin da ya dabaibaye hedikwatar hukumar.



Kwamitin ya kuma nuna damuwa cewa daga cikin naira biliyan 1.19 da hukumar ta kashe, an ware naira miliyan 943 domin biyan alawus ga mambobin kwamitin gudanarwa, abin da sanatocin suka ce bai dace da manufar ci gaban yankin ba.


Sai dai shugaban kwamitin gudanarwar NWDC, Abdullahi Lawal, ya kare kashe kuɗin, yana mai cewa an yi su ne bisa tanadin dokar kafa hukumar ta 2024. Ya ce kwamitin ya gudanar da taruka bakwai tare da amincewa da kudurori 63 domin kafa tsarin gudanar da hukumar.


Lawal ya kuma zargi mahukuntan gudanarwar hukumar da gaza aiwatar da wasu muhimman shawarwarin kwamitin, lamarin da ya ce ya janyo tsaiko wajen fara ayyukan hukumar yadda ya kamata.


Daga bisani, kwamitin Majalisar Dattawa ya shiga zaman sirri domin duba wasu takardu masu muhimmanci da kuma karɓar ƙarin bayani daga jami'an ma'aikatar raya yankuna da na hukumar.

Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org