An samu haɗarin gobara sau 30 da rasa rayuka 5 a watan Yuni a Kano - Hukumar Kwanakwana
Hukumar Kwanakwana ta Jihar Kano ta ce mutane biyar sun rasa rayukansu sakamakon gobara da sauran hadarurruka da hukumar ta gudanar a watan Yuni.
Hakan na kunshe ne cikin rahoton ayyukan watan da kakakin hukumar, Saminu Yusif Abdullahi, ya fitar.
Rahoton ya bayyana cewa hukumar ta kuma ceto mutane uku daga wasu hadarurruka daban-daban a cikin wannan lokaci.
A cewar rahoton, jami'an kashe gobara sun amsa kiran aukuwar gobara 30, inda ya kara da cewa sun kuma gudanar da ayyukan ceto guda bakwai a fadin kananan hukumomi 44 na jihar, yayin da aka samu kiran ƙarya guda daya.
Rahoton ya nuna cewa gobarar ta lalata kadarori da darajarsu ta kai naira miliyan 120.45, yayin da aka samu nasarar ceto kadarori da darajarsu ta kai naira miliyan 481.8 sakamakon gaggawar da jami'an kashe gobara suka yi.
Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Alhaji Sani Anas, ya bukaci al'umma su rika yin taka-tsantsan wajen amfani da wuta tare da tabbatar da cewa an kashe duk wata wuta bayan an gama amfani da ita domin kauce wa gobara.
Ya kuma shawarci iyaye da masu kula da yara da su nisanta yara daga kududdufai, tafkuna, koguna da rijiyoyin da ba a rufe ba domin rage yawan mace-macen nutsewa cikin ruwa, musamman a tsakanin yara da matasa.
