Ƙaramar Hukumar Katsina Ta Ɗauki Nauyin Karatun Dalibai 200 Kyauta
Shugaban Ƙaramar Hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya amince da ɗaukar sabbin ɗalibai 200 da suka kammala sakandare cikin shirin tallafin karatu na ƙaramar hukumar.
A ƙarƙashin shirin, ɗaliban da suka yi nasara za su yi karatu a Hassan Usman Katsina Polytechnic (HUK) da kuma Katsina State Institute of Technology and Management (KSITM), inda ƙaramar hukumar za ta ɗauki nauyin kuɗin karatunsu gaba ɗaya.
A cewar ƙaramar hukumar, an ƙirƙiri shirin ne domin tallafa wa ɗaliban da suka cancanta, musamman waɗanda suka fito daga iyalai masu ƙaramin ƙarfi da ke fuskantar ƙalubalen ci gaba da karatu saboda rashin kuɗi.
Ta ce shirin na daga cikin ƙoƙarin bunƙasa ilimi, bai wa matasa dama, da kuma zuba jari wajen haɓaka albarkatun ɗan Adam a faɗin Ƙaramar Hukumar Katsina.
Ƙaramar hukumar ta ƙara da cewa za ta sanar da yadda za a nema, sharuɗɗan shiga da kuma ranar fara karɓar takardun neman tallafin ta hanyoyin sadarwarta na hukuma.
