Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya: Gwamnatin Nijeriya ta nemi haɗin gwiwa don yaƙi da yaɗa labaran ƙarya
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta buƙaci a ƙara haɗin gwiwa tsakanin kafafen yaɗa labarai, hukumomin gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki domin magance barazanar yaɗa labaran ƙarya.
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja yayin bikin Ranar ’Yancin ’Yan Jarida ta Duniya ta shekarar 2026 da aka gudanar a Radio House.
Ya ce: “Wannan gwamnati ta ba da fifiko ga haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki a kafafen yaɗa labarai da kuma abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa domin inganta aikin jarida mai inganci da kuma yaƙi da yaɗa labaran ƙarya.”
Ya bayyana ’yancin ’yan jarida a matsayin muhimmin haƙƙi da kundin tsarin mulki ya tanada, yana mai tabbatar da cewa gwamnati za ta ci gaba da samar da yanayi mai kyau da zai bai wa kafafen yaɗa labarai damar gudanar da aikin su cikin ’yanci, tsaro da gaskiya.
“Gwamnatin Tarayya ta amince da ’yancin ’yan jarida, kuma za ta ci gaba da samar da yanayin da zai bai wa kafafen yaɗa labarai damar yin aikin su cikin ’yanci, tsaro da gaskiya,” inji shi.
Ministan ya ƙara da cewa Gwamnatin Tarayya ta ɗauki matakai na ƙarfafa gaskiya da samun bayanai ta hanyar cigaba da hulɗa da kafafen yaɗa labarai, aiwatar da dokar ’Yancin Samun Bayanai, da kuma saka hannun jari a hanyoyin sadarwa na jama’a.
Ya kuma bayyana haɗin gwiwar Nijeriya da UNESCO wajen kafa Cibiyar Ilimin Kafofin Watsa Labarai da Bayanai ta Duniya (IMILI) a Abuja a matsayin wani muhimmin mataki na ƙarfafa ilimin kafafen yaɗa labarai da bayanai da kuma inganta sadarwa mai kyau a wannan zamani na dijital.
Ministan ya buƙaci ’yan jarida da su ci gaba da kiyaye ƙwarewa da ƙa’idojin aiki, yana mai jaddada cewa dole ne ’yancin aikin jarida ya tafi tare da ɗaukar nauyin da ya rataye a wuyan jama'a.
“Ainihin gwajin ’yancin ’yan jarida ba wai a cikin furucin mu yake ba, a cikin ayyukan mu yake, yadda ’yan jarida ke gudanar da aikin su cikin tsaro, yadda ake yaɗa bayanai cikin gaskiya, da kuma yadda jama’a suke amfani da su yadda ya kamata,” inji shi.
A nata jawabin maraba, Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Dakta Binyerem Ukaire, ta bayyana taron a matsayin wata dama ta ƙarfafa haɗin gwiwa da inganta wayar da kan jama’a.
Ta yi kira da a ƙara haɗin kai tsakanin hukumomi domin magance ƙalubalen yaɗa labaran ƙarya, musamman la’akari da yadda kafafen sadarwa na zamani suke ƙara yaɗuwa.
Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyar ta ta ci gaba da aiki tare da masu ruwa da tsaki domin gina tsarin bayanai mai ƙarfi da zai tallafa wa dimokiraɗiyya, haɗin kan ƙasa da cigaba mai ɗorewa.
Taron ya samu halartar Sufeto Janar na ’Yan Sanda, wanda jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, DCP Anthony Okon Placid, ya wakilta; da Darakta-Janar na DSS, wanda Daraktan Tsare-Tsare, M.O. Chukwuka, ya wakilta; da Babban Sakataren Hukumar Kula da Aikin Jarida ta Nijeriya, Dakta Dilli Ezughah; da kuma Shugabar Ofishin UNESCO a Abuja, wadda Shugabar Sashen Sadarwa da Bayanai, Ms Yachat Nuhu, ta wakilta.

