Za a fitar da sunayen sabbin jakadu nan ba da jimawa ba amma shin an zaɓi ƙwararru ne ko dai siyasar abota ce ta sake yin tasiri?.karin bayani 👇
A cewar majiyoyin, an jima ana tantance sunayen manyan jami’ai da kwararru da za su wakilci Najeriya a manyan kasashe, kuma an ce lissafin ya kusa kammalawa. Wannan zai kasance muhimmin mataki na kafa sabuwar hanya tsakanin Najeriya da abokan hulɗarta na duniya, musamman a fannin tattalin arziki, tsaro, da bunkasar hulɗar kasuwanci.
Rahoton ya kuma nuna cewa wasu tsofaffin jakadu da wa’adinsu ya wuce za a maye gurbinsu, yayin da wasu sabbin fuska za su samu damar shiga sabuwar tafiyar diflomasiyyar gwamnatin Tinubu.
Ana sa ran sanarwar za ta fito a hukumance nan da makonni kadan, inda gwamnati ke fatan sabbin jakadun za su kawo sabuwar dabara da ƙwarewa wajen kare muradun Nijeriya a duk inda aka tura su
#NigeriaPolitics #Tinubu #ForeignAffairs #Diplomacy #Abuja #Ambassadors #VillaUpdate #NaijaNews #TrendingNaija #CeceKuce